Spread the love
Daga Aminu Abdullahi Gusau.
Tsohon gwamnan jihar Zamfara kuma jagoran jam’iyyar APC a  jihar, Alhaji Abdul Aziz Yari Abubakar ya sha alwashin  a zaben 2023 mai zuwa jam’iyyar su za ta lashe dukkan kujerun da za’a tsaya takara.
Yari yayi wannan bayani ne a garin Talatar Mafara dake jihar Zamfara, jim kadan bayan ya amshi rejistarsa ta zama dan jam’iyya wanda ke gudana a duk fadin jihar.
Ya ce daman jihar  ta APC ce a siyasance, domin tun lokacin da aka fara siyasa a shekara ta 1999, wannan jam’iyyar ita ke samun nasara a duk lokacin da aka gudanar da zabe.
“Kun ga tun tana APP, ta koma ANPP har yanzu data zama APC muke cin zabe, ko wannan zaben na 2019 mu muka samu nasara sai dai kawai ‘yan matsaloli na cikin gida da suka sa kotu ta karbe taba wata jam’iyyar.
 “A don haka muna kira ga magoya bayan mu da su fito kwansu da kwarkwatarsu su karbi katin zaman dan jam’iyyar APC, domin yin hakan zai bamu damar kada duk wata jam’iyya wadda zamuyi takara da ita.”inyi shi.
Jagoran na APC a jihar ta zamfara ya kara da cewa, yanzu duk an dunke matsalolin da aka fuskanta, a lokacin zaben 2019, yanzu duk an dunkule an koma tsintsiya madaurin ki daya.
Tsohon gwamnan dai ya karbi tashi takar dar rajistar a rumfar zabe mai suna rumfar malan Isa mai lamba 001, bisa ga kulawar kwamitin da aka turo daga uwar jam’iyyar APC, karkashin jagoran cin Alhaji Kareti Lawal,domin suga yadda rajistar za ta kaya a jihar Zamfara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *