Spread the love

Jam’iyar APC da sauran jam’iyyu 31  a Sokoto ba za ta shiga zaɓen ƙananan hukumomi da za a yi ba

Jam’iyar APC a jihar Sakkwato ta yanke hukuncin ba za ta shiga zaɓen ƙananan hukumomi da za a gudanar a jihar Sakkwato a wata maris mai zuwa ba.
Shugaban riƙo na jam’iyar a jihar Alhaji Isa Sadiƙ Achida ya sanar da haka a taron manema labarai da suka kira a sakatariyar jam’iyar dake kan titin Sarkin Musulmi Abubakar ya ce yanayin rashin adalci da ya bayyana karara kan kasawar gwamnatin jiha ga baiwa ƙananan hukumomi damar da ta dace da su, wannan abin baƙin ciki ne yanda ake sama da faɗi da dukiyarsu bayan rage wa’adin shugaban ƙananan hukumomi daga shekara uku zuwa biyu don kawai biyan buƙatar shugabanci ta ƙashin kai.
Achida ya ce bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki na jam’iya sun yanke shawarar ba za su shiga zaɓen da gwamnatin Sakkwato za ta gudanar ba.
Ya ƙara da cewar hukumar zaɓe ta jiha ya kamata ta kira jam’iyyu kafin ta shirya jadawalin gudanar da zaɓe rashin yin haka ke nuna ƙarara ba za su yi adalci ba don sun ƙi baiwa jam’iyu damar da ta dace da su.
Ya ce shugabanin  hukumar da gwamnatin Tambuwall ta naɗa  dukansu ‘yan jam’iyar PDP ne dake da katin jam’iya don haka ba za su yiwa APC adalci ba.
Achida ya ce APC nada farin jinin da za su iya cin zaɓe amma ko an yi nasara Tambuwal ba zai bari su yi aiki ba don gudun ɓata suna sun janye ba za su shiga ba.
Managarciya tana ganin yakamata jam’iyar ta shiga zaɓe ganin yanda magoya bayanta ke buƙatar hakan.
Ya ce sauran jam’iyun adawa 31 a jiha sun aminta ba za su shiga zaɓen ba kan rashin adalci da APC ta fahimta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *