Spread the love

 

Kungiyar ‘yan jarida masu aika da rahotanni a wajen Sakkwato waton correspondent chapel sun kauracewa dauka da buga duk wasu rahotanni daga fadar gwamnatin Sakkwato.

Bayanin wannan matakin na kunshe ne a cikin wata takarda da shugaban kungiyar Malam Habibu Harisu da Sakatare Mista Ankeli Emanuel suka sanyawa hannu aka rabawa manema labarai a jiha.

Kungiyar ta nuna ta dauki matakin ne kan wasu dalilai na musgunawa da ake yi wa mambobinta. “Biyo bayan walakanta mambobinmu a gidan gwamnatin jiha da jami’an tsaro suka yi a jiya jumu’a, mun yanke hukuncin kauracewa aiyukkan gwamnatin jiha gaba daya.

“Haka ma Kungiyarmu ta yanken hukuncin ba za ta sake daukar duk wani bayanin manema labarai da ya fito gidan gwamnatin jihar ba, kuma  wata kungiya ko daidaikun jama’a ko ‘yan siyasa da suka kasa gayyatarmu mu shedi abin da suka gudanar. a cewar bayanin.

Kungiyar ta yanke hunkuncin ne wani zaman gaggawa da ta gudanar a yau ta yi tir da halin jami’an tsaron gidan gwamnati da suke yi wa manema labarai barazana a lokacin da suka zo gudanar da aikinsu.

Sun yi kira shugabannin tsaro a jiha su fahimtar da jami’ansu dangantakar dan jarida da su.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *