Spread the love
Muhammad M. Nasir.
 Sanata Ibrahim Abdullahi Gobir ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta duba yiwuwar ƙaro ma’aikatan tsaro a yankunan jihar Sakkwato.
Sanata Gobir ya yi wannan kiran ne a wani bayani da ya fitar ga manema labarai wanda mataimakinsa kan yaɗa labarai Bello Muhammad ya sanyawa hannu a ranar Jumu’a ya koka kan yadda harkokin ɓata gari da mahara ke ta’azara a ƙananan hukumomin  Sabon Birni da Illela da Isah da Wurno da Raɓah da Gwadabawa da Gada da Goronyo.
Ya ce jami’an tsaron da ke ƙananan hukumomin ba su isa ba, akwai bukatar ƙari domin ba wata ƙaramar hukuma da ke da jami’in ‘yan sanda sama da 100.
Abdullahi Gobir ya roƙi gwamnatin tarayya ta turo a ƙalla jami’an ‘yan sanda 200 tare da kayan aiki da Hilux 10 domin tabbatar da kiyaye rayukka da dukiyoyin jama’a.
Sanata wanda shi ne shugaban kwamitin majalisar dattijai kan tsaron ƙasa da bayanan sirri ya nuna damuwarsa kan tsare rayuwa da dukiyoyin ‘yan kasa.
Managarciya ta samu labarin ya jajantawa mutanrn kauyen Lugu a ƙaramar hukumar Wurno kan harin ‘yan ta’adda da aka kawo masu kwanannan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *