Spread the love

 

Daga Muhammad M. Nasir.

 

Ministan Lamurran ‘yan sanda Muhammadu Maigari Dingyadi Katukan Sokoto  ya sabunta rijistarsa ta zama mamba na jam’iyyar APC ya yi kira ga magoya bayansu da su fito su yi zabe a zavben kanan hukumomi da gwamnatin Sakkwato za ta gudanar a jiha, yana da tabbacin jam’iyarsu ta APC za ta samu nasara a zaben.

“Jam’iyarmu ta APC a jiha za ta shiga zaben kananan hukumomi da za a gudanar.” A cewar Ministan ‘yan sanda.

 

 

Ministan ya karbi katinsa a rumfar  003 Asibiti shiyar Magaji, a Mazabar Dingyadi/Badawa a karamar hukumar mulki ta Bodinga  a Sakkwato.

Farfesa Saleh Galadima Kanam shugaban kwamitin bayar da katin a jiha ne da jami’in rijistar Bashiru Usman Dingyadi suka yi hidimar yi wa minista rijista,  ya bayyana aikin  abin karfafawa ne.

 

Ya godewa jama’ar jihar Sakkwato Kan goyon bayansu ga  gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Ya yi kira da jama’a su fito su yi rijistar domin kara samun magoya baya ga jam’iyar.

[everest_form id=”5″]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *