Spread the love
An hana ma’aikatan Majalisar dokokin Zamfara yin zanga-zangar lumana
Ma’aikatan Majalisar na ihar Zamfara sun so su yi Zanga-Zangar lumana a kan Wasu hakkokinsu da Gwamnati ta hana masu.
Ma’aikatan sun koka akan akwai Kudaden HAZARD da ake biyan Ma’aikatan duk Shekara, amma an daina ba su duk da an yi ta ba su baki Za a basu, har aka kaisu bango.
An Samu hana Ma’aikatan su yi Zanga-Zangar, lumana kamar yadda suka tsara.
Ma’aikatan suna son a biya su saboda majalisar ƙasa ta ce a biya ma’aikatan haƙƙinsu da ake ba su tin farko aka daina daga baya.
Ma’aikatan sun haƙura da yin zanga-zangar sun koma kan aikinsu yanda yakamata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *