Spread the love
Gwamnatin Sakkwato a ƙarƙashin gwamna Aminu Waziri Tambuwal ta soke wasu aiyukka da gwamnatin Sanata Aliyu Wamakko ta bayar a lokacin gwamnatinsa.
A zaman da majalisar zartarwa ta jiha  ta yi a jiya Laraba ta soke kwanhilar aiyukka biyar da aka fita batunsu.
Huɗu daga cikin aiyukkan da aka fita batunsu ɗan kwangila ya watsar da su, suna a cikin asibitin Murtala Muhammad sun  haɗa da ƙarin gina babban  ɗakin jinya guda biyu da fitar da wurare a cikin asibitin da gina gidajen ma’aikata 47 da kammala wasu aiyukka na musamman da suka ƙunshi wurin fiɗa, ɗakin ajiye gawa, wurin wanki dasauransu.
Haka ma Tambuwal ya soke kwangilar gina asibitin Wamakko da aka ba da  kwangilarta tun a shekarar 2013 a gwamnatin Sanata Wamakko kenan.
Kwamishinan lafiya Dakta Ali Muhammad Inname ya ce soke kwangilar asibitin Murtala ta faru ne kan fita batun aikin da dankwangila ya yi.
Ya ce za a bi  ka’idodin doka kafin sake ba da kwangilar ga wasu ‘yan kwangila da suka shirya.
Ya ce asibitin Wamakko ita ko da jimawa an baiwa wani kamfani aikin.
Hakan ke nuna an ba da aikin asibitin kafin zaman majalisar zartarwar jiha.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *