Majalisar Dattawa ta yi Kira da Gwamnatin Tarayya ta  dubi yarjejeniyar Shiga da fice ta ECOWAS
Daga M. A. Umar, Minna
Majalisar dattawa, a ranar Larabar makon nan tayi kira ga gwamnatin tarayya da ta sake bitar yarjejeniyar shige da fice tsakanin mutanen kasashen Afrika ta yamma domin shawo kan kwararowar masu aikata laifuka cikin kasar nan.
Kiran na majalisar ya zo a daidai lokacin da shugaban ta, Dakta Ahmad Lawan yayi gargadi akan cusa kabilanci a harkar garkuwa da mutane da yan bindiga dadi.
Majalisar tayi kiran ne bayan doguwar tattaunawa akan kudurin rashin tsaro a fadin Najeriya.
Da yake gabatar da kudurin, Sanata Robert Ajayi Boroffice na jam’iyyar APC daga jihar Ondo, yayi nuni bisa rahotannin kashe jama’a da garkuwa da su a jihohin Ondo, Edo, Oyo, Imo, Kaduna, Zamfara, Niger, Nasarawa, Kebbi da wasu jihohin kasar nan.
Majalisar ta kuma bukaci mai ba shugaban kasa shawara kan harkar tsaro, da sababbin hafsoshin soja da babban sufeton yan sanda na kasa su gano hanyoyin canza fasalin tsarin tsaron kasar nan da yadda ma’aikatan tsaro zasu samu azamar shawo kan matsalar musamman a kauyuka.
Majalisar tayi kira ga gwamnonin jihohi da su farfado da ingataccen yanayin mulki a kauyuka da kuma jawo al’ummar su wajen magance rikicin kabilanci da kaddamar da shirin kiwo na zamani domin magance rikice-rikcen makiyaya da manoma.
A yayin da ta ke bukatar jami’an tsaro su yi amfani da jiragen sama marasa matuka da jiragen helikwafta wajen lura da dazuzzuka domin gano mafakar yan bindiga, majalisar dattawan tayi kira ga gwamnatin tarayya da ta dauki matakin gaugawa don magance safarar makamai da tabbatar da dokar hana mallakar makamai ba bisa ka’ida ba.
A yayin jawabin sa, shugaban majalisar, Dakta Ahmad Lawan ya gargadi yan siyasa da su guji mai da rashin tsaro na kabilanci saboda kauce ma kawo rikicin da zai kai ga zubar da jini tsakanin kabilun kasar nan.
Lawan yayi kiran samar da karin kudade ga sojoji don su samu damar shawo kan matsalar rashin tsaro da ta mamaye dukkan sassan kasar nan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *