Spread the love

Wani matashi mai shekara 35 Muhammad Faruk yana cikin komar rundunar ‘yan sandan jihar Yobe kan zarginsa da yi wata tsohuwa fyade.

Lamarin ya faru a garin Gadaka in da  dukan su biyun suke zaune, kamar yadda mai magana da yawun ‘yan sanda Dungus Abdulkarim ya fadi.

A bayanin da ya yi ya ce wanda ake zargi ya amsa laifinsa kuma a binciken kiyon lafiya da aka yi ya nuna ya shiga cikinta.

Hukumar ‘yan sanda ta kudiri kawo karshen irin wannan rashin hankalin da ake yi wa yara kanana da manya.

Bayanin da ‘yan sanda suka fitar ga manema labarai ya nuna cewa Muhammad  Faruku Gadaka mai shekara 35 ya yi wa tsohuwa mai shekara 90 fyade  a garin na Gadaka binciken kiyon lafiya ya nuna hakan, amma dai har yanzu ana kan bincike.

Hukumar ta nuna jindadinta ga mutanen Yobe kan hadin kan da suke ba su a lokuttan aikinsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *