Daga karshe dai Maryam Malika ta bayyana matsayin aurenta a wata takarda data wallafa.

An ga fom na zama ‘yar wasan Hausa da ta cike wanda hakan ke nuna ita ta dawo harkar wasan Hausa gadangadan.
Maryam a lokaci guda ta shahara a masana’antar Kannywood kai tsaye kuma ta bari ta yi aure abin da ya yi matuƙar girgiza masoyanta tare da faranta musu.
 

A kwanakin baya an samu rahoton cewa auren Maryam Malika ya mutu  har kafafen sadarwa da yawa sun wallafa wannan maganar.

Ana cikin hakan kwatsam kuma sai mijinta ya fito karyata wannan batu inda yace aurensu na nan daram dam da shi da ita. Sai dai kuma bai dade da yin wannan furuci ba sai gashi mun samu labari daga shafin jarumar ta wallafa za ta fito cikin wani sabon film Mai dogon zango wanda kamfanin shareef studio ke gabatarwa wanda Abdul M Shareef ya shirya wannan fim mai dogon zango mai suna  ”Da ace ba zuciya”.

Hakan ke nuna cewa ta dawo cikin harkar gadangadan kuma aurenta da aka ba da labari ya mutu gaskiya ne.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *