Spread the love
Malami ya sabunta rijistarsa ta APC ya faɗi dalilin da ya sa Kebbi take gaba a jihohin APC
Muhammad M. Nasir
Ministan Shari’ar Nijeriya Babban lauya Abubakar Malami ya sabunta rijistar jam’iyarsa ta APC a Talatar nan.
Wannan na ƙunshe ne a cikin jawabin da mataimaki na musamman ga Minista kan yada labarai da hulɗa da jama’a Dakta Umar Jibrilu Gwandu, ya fitar ga manema labarai.
A cewarsa bayan ya karɓi katinsa a rumfar Filin Mariya Nasarawa 1 a ƙaramar hukumar Birnin Kebbi a jihar Kebbi ya yi kira ga masu son shiga jam’iyar da waɗanda za su sabunta su hanzarta su je su karɓa a ko’ina cikin Nijeriya.
Ya ce aikin na buƙatar gudunmuwa da goyon bayan kowane ɗan jam’iya domin ƙarin samun haɗin kai, yin dimukuraɗiyyar cikin gida tana da amfani ga cigaban ƙasa.
Malami ya ce APC tana bugun gaba da jihar Kebbi domin ita ce kaɗai a Arewa maso yamma ba ta da ƙalubalen jefa kuri’a a 2019 kuma aka ƙara samun yawan masu jefa ƙuri’a fiye da na 2015.
A bayanin ya ce gwamnatin tarayya wadda APC ke jagoranta ta gudanar da aiyukkan cigaba a ƙasa musamman a jihar Kebbi.
Ya ce da gudunmuwar gwamnatin tarayya a wurin samar da shinkafa Kebbi na cikin jihohin da gwamnati ta samun kuɗin shiga da yawansu ya kai biliyan biyar kan fitar da shinkafa.
Ya nemi jagorori a jihar su taimaka a samu nasarar kamala aikin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *