Spread the love
An yi nasarar kama wanda ake zargi da hada baki a sace matar yayansa
Kungiyar ‘yan sakai a garin  Zariya sun damke wasu mutane uku da ake zargin su ke ba masu garkuwa da mutane da kuma ‘yan ta’adda bayanai a yankin Dutsen Abba ta Karamar hukumar Zariya.
Wadanda aka kama sun hada da Mu’azu Sani wanda  kanin Kansila AbdulAzeez ne wanda aka dauki matarsa sai Mubarak Adamu mai shekaru 20 da ke Anguwar Makada da Faisal wanda  Bafillatani ne shi ma mazaunin Anguwar Malam Atiku da ke gundumar Dutsen Abba.
A ranar 4 ga watan fabrairu da ya gabata da dare wasu ‘yan bindiga da ba a san yawan su ba dauke da bindigogi kirar AK 47 suka afkawa kauyen Unguwan Hazo dake gudumar Dutsen Abba a karamar hukumar Zariya inda suka kashe wani mai suna Musa Isa dan shekara 28 da haihuwa da Yusuf Sulaiman mai shekaru 30 da haihuwa, ya yin da aka harbi matan aure 2 Fatima Sulaiman  da aka fi sani da suna Magajiya mai shekaru 64 da haihuwa da Hafsatu Isa da aka fi sani da suna Uwa mai shekaru 50 wanda yanzu haka suke kwance a asibitin kauran Wali Zariya.
Maharan sun kai hari ne kauyen domin kwace babura kirar Boxer guda 4, daga a gidan wani kansila mai suna Abdulaziz Sani, kansila mai wakiltar gundumar Dutsen Abba a kauyen anguwar Makada in da suka  sace  matar kansila mai suna Samira Abduaziz da wata matar aure mai suna Halima M Sani.
‘Yan sa kai sun samu nasarar kwato wadanda aka sace da wasu kaya kafin daga bisani su samu nasarar kama wadanda ake zargi da kwarmata bayani ga masu garkuwan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *