Spread the love

Yakamata Wamakko ya sani haƙƙin musulunci yafi na siyasa—-Salame

Muhammad M. Nasir.

Honarabul Abdullahi Balarabe Salame ya godewa Kakakin majalisar wakillai ta kasa Femi Gbajabiamila kan ziyarar jaje da ya kawo masa a gidansa bayan da ya ketare rijiya da baya a wani farmaki da ‘yan bindiga wadanda ake kyautata zaton ‘yan fashi ne.

Salame ya godewa Gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal da Sarkin musulmi kan kulawarsu ga abin da ya same shi.

Haka ma ya godewa ‘yan majalisar tarayya na jihar Sakkwato amma ‘yan jam’iyar PDP domin su ne suka jajanta masa kan lamarin da bai ji ciwo ba.

“Muna gode masa(Femi) saboda ya yi aiki da musulunci, ko ‘yan uwana da suke nan Sakkwato a jam’iyar APC da jagoran jam’iyar Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko bai zo ba bai aiko ba, ya nuna Femi musulmi ne da ya san ka’ida ta musulunci da ya zo ya dauke hakkin musulunci, sauran da ba su dauke hakki ba Allah ya shirye su su gane musulmi nada hakki ga musulmi fiye da siyasa da komi.

“Ina godiya ga malamai da limamai da kowa da suka yimin jaje wadan da ba su yi ba ya nuna sun ji dadi tau Allah ya shirya su” a cewar Honarabul Salame.

A jawabin jaje da Kakakin Majalisar ya gabatar ya ce da yanda aka yi bayanin farmakin ‘yan bindiga ne suka zo sai dai Allah ya tsare ba abinda ya faru.

Ya ce na zo nan ne domin na taya dan uwa aboki na tare dani jajen abin da ya same shi da fatar Allah ya tsare gaba ka ci gaba da addu’a Allah yana karbar addu’arka. a cewarsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *