Wahalar man fetur ta kunno kai a Nijeriya

Wahalar man fetur ta kunno kai yayinda manyan diloli masu rumbu ajiye man na ‘yan kasuwa suka rufe sayar da man fetur

Alhaji Abubakar Maigandi Shugaban kungiyar masu dakon man fetur  a kasa ya mambobin nasu sun rufe rumbunansu ne kan maganar da suke ji tana yawo farashin man fetur zai daga sama.

Duk wannan jita-jitar hukumomin da lamarin yake kansu har yanzu ba su bayar da sanarwa Karin man ga dilolin a kowane mataki ba.

Da yake Magana da manema labarai daya daga cikin wadanda suka mallaki rumbun ajiye mai ya ce ya riga ya kara farashin mansa da naira 7

Mataimakin shugaban masu rumbun a kasa (Depot) ya ce rubunan ajiye mai sun kara farashin sayar da mansu daga 148 zuwa 155

Ya ce masu rumbun mai sun rufe wurarensu ne saboda tsammain Karin kudin Fetur

Kungiyar masu sayar da man Fetur IPMAN har yanzu ba ta umarci mambobinta su kara kudin mai a gidajen sayar da fetur ba don har yanzu ba su tabbata ko masu rumbunan fetur sun kara farashi a saman doka ko akasin haka ba.

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *