Spread the love
Gawurtaccen Dan ta’adda ya mika Bindiga 22, da dubban albarussai ga Gwamnatin Zamfara
Daga Aminu Abdullahi Gusau.
Shirin gwamnatin Zamfara na sulhu tsakanin ta da yan ta’adda yana cigaba da haifar da da mai ido, domin a yau wani shararren Dan ta’adda mai suna Awwalun Daudawa ya mika wa gwamnatin bindigogin sa har guda ashirin da biyu.
Awwalun Daudawa, yana daya daga cikin manya manyan yan ta’addan da suka addabi dajin Dumburum da kuma Gidan jaja a cikin karamar hukumar mulkin Zurmi.
Da yake karbar makaman gwamna Bello Muhammed Matawalle yace, hakika wannan Awwalun Daudawa, ya karba kiran da malamai keyi masu nasu ajiye makaman su, su shigo cikin jama’a domin samun zaman lafiya mai dorewa a fadin jihar zamfara da kewaye.
Yace, kafin a samu shawo kansa, sun kwashe sati ukku suna tattaunawa dashi, kuma tattaunawar ta haifar da da mai ido.
“Mu munyi imani da cewa sulhu alhairine saboda haka ba zamu damu da duk wanda ke ganin hakan bazai yiwuba, domin munayi ne tsakanin mu da Allah domin mu saukar da amanar da Allah ya bamu ta kula da mutanen da muke mulki da kuma  dukiyoyin su.
” Saboda haka duk wanda ke ganin sulhu bazai yiwuba ya rage nashi, kuma ina kara godiya ga malaman mu da limaman mu da kuma jami’an tsaron mu bisa ga na mijin kokarin da suke yi ba dare ba rana domin samun zaman lafiya a zamfara”.inji shi.
Gwamna matawalle ya kara da cewa, wannan da ya kawo makaman sa kuma yace ya rungumi zaman lafiya to za’a samar mashi abunyi, kamar sashi makarantar boko data muhammadiyya kamar yanda ya roka.
Shima da yake nashi jawabin  Awwalun Daudawa yace, shi ya yanke shawarar aje makaman sane bisa ga la’akari da cewa sulhu shine hanya mafi kyawo na zama lafiya, ya kara da cewa kuma shi yayi alkawari harga Allah bazai sake komawa wannan harkar banza ba.
Daganan ya roki gwamnati data samar mashi muhallin dazai zauna kuma tasashi makaranta boko da muhammadiyya domin ya cigaba da wata sabuwar rayuwa, kuma ya roki duk wanda ya cutar da ya yafe masa.
Bayan sa akwai yaran sa su biyar da suma suka biyoshi domin suma sun gano cewa sulhu nan shine mafita.
Daga karshe an basu rantsuwa da Alkur’ani mai girma kuma sun rantse bazasu sake yin sata, ko garkuwa mutane ba.
Anyi wannan gagarumin bukin ne a fadar gwamnatin jihar Zamfara a gaban shugabannin jami’an tsaro dake wannan jiha, da kuma manya manyan jami’an gwamnati.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *