Spread the love

Akalla mutum daya ne aka kashe mutum biyu suka samu rauni a rigimar da ta kaure tsakanin matasa ‘yan bangar siyasa dake jam’iyu biyu na hamayya cikin karamar hukumar Babura a jihar Jigawa.

Babura mahaifar gwamnan jihar Jigawa ce Muhammad Badaru Abubakar, rigimar ta kaure a wurin kaddamar da aikin hanya a karamar hukumar da kudinsu ya kai 3.9 biliyan.

Mai magana da yawun ‘yan sanda a jihar ya ce ba wata rayuwa da ta salwanta amma ya tabbatar da samu rauni.

Ya fadi sunayen wadan da suka samu rauni Sadisu Muhammad da Abubakar Mahmud.

Ya ce lamurra sun dawo daidai ‘yan sanda a karamar hukumar sun yi aikinsu.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *