Spread the love

Sabuwar rigima ta kunno kai a jam’iyar APC kan wanda zai jagorance ta a kasa wasu jagorori a daya daga cikin jam’iyun da suka samar da APC waton CPC suna son shugaban jam’iyar APC ya fito daga bangarensu .

Dalilansu dukan jam’iyun da suka samar da APC su uku sun jagorancin jam’iyar bancinsu tun sanda shugaba Buhari ya zama shugaban kasa ba su rike wannan kujerar ba.

Tun da har Buhari zai kammala wa’adinsa a 2023 a baiwa bangarensu wannan damar ta jagorancin jam’iya abu ne da yakamata a wurin raba daidai.

Bangaren Arewa ta tsakiya suna rokon a bari su samar da shugaban bangaren sun zargi tsarin shugabancin jam’iya tun a 2014 ana danne su, an fahimci tsoffin gwamnonin Nasarwa Sanata Abdullahi Adamu da Sanata Umar Tanko Almakura suna son a ba su damar jagorancin daga bangarensu.

Tsoffin gwamnonin biyu sun shiga cikin jerin wadanda ake yada cewa suna son shugabancin jam’iyar waton Abdul’aziz Yari da Kashim Shattima da Ali Modu Sharif da Clement Ebri.

Duk da hakan dai masu nema na duba yanayin in da shugaba Buhari ya sa gaba kan wanda yake so ya jagoranci jam’iyar, shugaban jam’iya da mukarabansa ana sa ran a zabe su a babban taron jam’iya a watan Yuni na wannan shekara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *