Spread the love
  • Duk wani mai son cigaban Nijeriya muna kira gare shi da ya je ya karbi katin APC da aka fara rabawa—-Honarabul DanFulani

Daga Muhammad M. Nasir

 

Bayar da katin jam’iyar APC da aka soma rabawa a dukkan jihohin Nijeriya, in da wasu za su sabunta katin wasu kuma su karbi sabo domin da shi ne za a yi zaben shugabannin jam’iya a wannan shekarar.

Jigo a jam’iyar APC Honaraabul Sanusi Danfulani ya yi kira ga duk musu son cigaban Nijeriya da suka isa jefa kuri’a su yi amfani da damar domin ta hakan ne za su iya zabar shugabanni masu kirki da suka cancanta su ja ragamar mulkin jama’a.

Honarabul a zantawarsa da Managarciya ya ce jam’iyar APC ita ce jam’iya mafi karfi da farin jini da tarin magoya baya a duk Afirika, wannan rijistar ne za ta kara fito da karfin jam’iyar a sarari, tunanin yin wannan aikin a wannan lokacin abin da yakamata ne da yabawa wadanda suka zo da tunanin.

“A matsayina halastaccen dan jam’iyar APC na gamsu da yanda shugaban riko na jam’iyar Gwamnan Yobe Mai Mala Buni ke tafiyar jagorancinsa hakan ke nuna mana zai kara daura jam’iyar bisa ga wata turba da za ta kara sanya a samu nasara a zaben 2023.” in ji Danfulani.

Ya ce a Sakkwato jagoran tafiyar jam’iyar Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko yana kokari sosai wurin inganta jam’iya abin da ya sa har yanzu ita ce jam’iya mafi rinjayen magoya baya da karbuwa a jihar.

“Biyayyarmu ga jagoranmu tana nan sai abin da ya ci gaba, duk wasu masu son kawo wani tarnaki ko mayar da tafiya baya ba za mu kyale su ba domin cigaban Sakkwato da al’ummarta ne gabanmu, hakan ya sa muke biyayya ga Sanata Wamakko don ba ya da wani buri da ya wuce cigaban jiharmu da kasa baki daya.” a Cewar Danfulani.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *