Spread the love

 

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya ayyana dokar hana tayar da zaune tsaye da sunan Bangar siyasa a karamar hukumar Gwoza.

Gwamnan ya bayyana dakatarwar ne a ranar Juma’a a fadar Sarkin Gwoza lokacin da ya kai ziyarar ban girma ga sarkin, yayin da yake aiki a karamar hukuma.

Gwamnan ya nuna rashin jin dadinsa game da halin matasa a  ya gargadi ‘yan siyasa masu haifar da‘ yan daba da su daina irin wannan dabi’ar.

 

“Ba na son irin wannan ɗabi’ar, bari mu yi ƙoƙari sosai don kauce wa tsunduma waɗannan matasa cikin ɓarnar siyasa.”

“Ku ‘yan siyasa ku ne kuke sa su  irin wannan ɗabi’a mara kyau, bari in faɗi gaskiya a gare ku, ba sai  ta wata hanya ne za a nuna farin jininku ba. Ko kadan wannan halin na sanya matasa bangar siyasa baya burgeni, b azan goyi bayan duk wanda yake son lalata makomar matasanmu ba, dole ne abar wannan lamarin a Borno”

“Na haramta barace-barace a cikin Maiduguri a  Biu, Gwoza  ma. Ina gargadi  da sanar da jama’a  daga gobe(Assabar) na umarci jami’an tsaro da su kamo duk wani da ke ake ganin   dan daba ne na siyasa.” A cewar  Zulum.

Wannan mataki nasa, da sauran gwamnonin Arewa za su yi koyi da shi, su kashe bangar siyasa da harkokin dabanci a tsakanin matasa ba karamin taimako ba ne ga al’ummar Nijeriya musamman Arewa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *