Spread the love
Shugaban Majalisar Dattijai ya miƙa saƙon ta’aziya bisa rasuwan wakilin muryar Amurk, Ibrahim Abdulaziz.
Daga M. A. Umar, Minna
A saqon sa na ta’aziya Dr Ahmad lawal ya bayyana kaxuwar sa da samun labarin rasuwan wakilin muryar Amurka a jihohin Adamawa da Taraba, Ibrahim Abdulaziz wanda ya rasu a ranar Juma’ar nan.
Shugabam majalisar ya bayyana marigayin a matsayin haziqin xan jarida da ya bada gudumawar sa wajen cigaban aikin jarida a ciki da wajen Najeriya.
Dakta Ahmad Lawal ya kuma bayyana marigayin a matsayin abun koyi gana baya, musamman matasa. Yace muryar Amurka dama sauran kafofin yaxa labarai za su yi rashin wannan jan gwarzo a aikin radiyo na qasa da qasa.
Shugaban majalisar ya bayyana jajen na sa ne a wata takardar manema labarai da ofishin da ke kula da harkokin yaxa labarai na ofishin sa ta fitar.
A ƙarshe Dakta Lawal yayi fatan haƙuri ga iyalai da yan uwa da abokan aiki da fatan Aljanna ta kasance makoma a gare shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *