Spread the love

 

Daga Muhammad M. Nasir

 

 

Kakakin majalisar dokokin jihar Sakkwato Honarabul Aminu Muhammad Acida wanda a halin yanzu ɗan jam’iyar APC ne da yake waƙiltar karamar hukumar Wurno a majalisar dokokin jiha, alamu sun ƙara bayyana da wuya ya zauna jam’iyarsa da ta yi masa riga da wando ganin yanda yake wasan ɓuya da jagorori da magoya bayan jam’iyar a duk sanda haɗuwa wuri ɗaya ta taso yakan sha jinin jikinsa ya ƙi zuwa ba tare da wani dalili da ake sanarwa mutane ba.

Jam’iyar APC a ranar Alhamis data gabata ta yi taron masu ruwa da tsaki domin aikin da ta sanya a gaba na sabunta katin jam’iya ga wanda yake da shi, da kuma yin sabo ga wanda bai da shi, a wurin taron kusan kowa ya zo wanda bai halarta ba ya ba da nasa uzuri amma babu wani saƙo daga Kakakin majalisar wanda hakan ƙarara yana nuna cewa jam’iyar ka da ta jira shi a wurin yanke kowane hukunci nata, ko da korarsa za a yi kafin ficewarsa, wanda hakan na nuna cewa ya kai mataki na ƙarshe da zai yi wa jam’iyar sallamar bankwana.

A wurin taron Managarciya ta zanta da ɗaya daga cikin jigo a jam’iyar da ya nemi a sakaya sunansa ya ce su sun riga sun ƙare da Kakakin majalisar tun lokacin da ya bijirewa jagoran tafiyarsu Sanata Aliyu Wamakko, ya yi gaban kansa domin son muƙami ya samu kuma, don haka babu wani dalili da zai sa ya rika cigaba da yaudarar kansa da sunan siyasa ce yake yi, wane ɗan siyasa ne zai kai irin matsayi na shugaban majalisa ya riƙa wasa da hankalinsa ba  ya shiga kowane taro na PDP ba ya zuwa na APC kuma har ya ga siyasa ce yake yi don kawai yana kallon kansa wanda yafi kowa tunani.

Ya ce “Ka san duk wanda ba ka gani a taron yau ba, kuma bai sanar da uzurinsa ga shugabanni ba da wuya a bashi katin jam’iyarmu don tun a wannan taron ya kori kansa, ba za ka ce ba ka iya hada fuska da jagororinmu kuma daga baya ka zagaya wurin waɗanda aka sanaya aiki ka ce su baka kati sannan ka yi tunanin suma irinka ne su ɗauki kati su baka hakan zai yi wuyar gaske” a cewarsa.

Jigon ya ce ka ga ai jagoran mambobinmu a majalisa shi ne ya jagoranci ‘yan uwansa ya yi magana a madadinsu don shi munka sani.

Managarciya ta so jin ta bakin Kakakin majalisar sai dai haƙar ba ta cimma ruwa ba.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *