Spread the love

Gwamnan jihar Borno ya a jiya Juma’a ya bayar da motoci bus 90 da za su iya daukar mutane 2,740 domin bunkasa harkar sufuri ga kamfanin zirga-zirga na jihar Borno.

Motocin sun hada da bus 40 mai daukar mutum 50 da 50 mai daukar mutum 14, akwai sabbi cikinsu da sha jiki.

Zulum ya raba motocin a filin wasa na Ramat wanda ma’aikatar zirga-zirga ta shirya kuma ita ce mai kula da kamfanin na Express mallakar jiha.

Ya yi kira da kamfanin ya ya tabbatar da gyaran motocin domin su zama koyaushe suna aiki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *