Spread the love

Zaɓen ƙanan hukumomi: Sakkwato ta Arewa na buƙatar jajirtacce kamar—– Dan galadiman  Jarman Sakkwato

Muhammad M. Nasir.
Alhaji Kasimu Ummaru Kwabo ɗan galadiman jarman Sakkwato jigo a jam’iyar PDP ya yi magana kan zaɓen ƙananan hukumomi da za a yi a Sakkwato ya fito ƙarara ya bayyana wanda yake da tabbas kan in an zaɓe sa a ƙaramar hukunarsu ta Sakkwato ta Arewa lalle za a samu cigaba.
Kasimu ya yi kalaman ne a zantawarsa da manema labarai a birnin jiha kan zaɓen ya ce matsayin Sakkwato ta Arewa cibiyar jiha kusan dukkan jagororin daular Usmaniya Sarkin musulmi da Waziri da sauransu a nan suke ana buƙatar samun jajirtacce da zai jahorance ta.
“A dukkan mutum biyar da ke  neman kujerar a PDP nafi ganin cancantar  Umar Muhammad(DG) don shi ne tsohon malamin makaranta, ma’aikacin gwamnati da ya kai matakin DG kuma ɗan siyasa yana da ƙwarewa a harkar tafiyar da al’umma da aikin gwamnati, ya san abin da ya kamata zai ciyar da ƙaramar hukumar da jiha a gaba.
“Umar jajirtacce ne zai rike amanar ƙaramar hukuma da girmama shugabanni, zaɓarsa alheri ne ga PDP musamman in da aka nufa gaba, da  zaɓen 2023 ke tunkarowa, in aka yi kuskuren haka mu magoya bayan PDP ba mu san in da za mu sanya kanmu ba.” a cewar Dangaladima.
Ya yi kira da mutane su daina siyasar kuɗi lokacin haka ya wuce a rungumi siyasar ‘yanci su zaɓi wanda ya cancanta shi ne suke da ta cewa kansa ba wanda aka zaɓa don wani abu ba.
Ya kuma shawarci Gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ganin shi gwamnan jama’a ne yasan abin da yake yi lauya ne ya yi amfani da zaɓin jama’a kar ya yi gaban kansa shi kaɗai.
“Duk wanda Allah ya baiwa nasara za mu goya masa baya don cigaban Sakkwato.” a cewarsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *