Spread the love
Mahaifiyar shugaban hukumar Zakka da waƙafi  ta rasu da shekara 111 a duniya
Daga Muhammad Nasir
Hajiya Fadimatu wadda aka fi sani da Igen Maidoki mahaifiya ce ga shugaban hukumar Zakka da Wakafi na jihar Sakkwato ta rasu bayan kwashe shekara 111 a duniya.
Hajiya Fadimatu dattijuwa ce a cikin al’umma ta rasu bayan doguwar jinya da ta yi.
Margayiyar tana da alaka da dangin Ummaru Mu’alkammu iyalin ne ke rike da sarautar Magajin Rafin Sakkwato, mahaifinta shi ne Malam Abdulkadir wanda aka fi sani da jikan Bahago, masaniyar addini ce kamar mahaifiyarta Malama Yatu.
 A tabakin jikarta Abdurrahem Lawal Maidoki ta bar ‘ya’ya bakwai cikinsu har da mahaifinsa shugaban hukunar zakka da wakafi na jihar Sakkwato Mihammad Lawal Maidoki(Sadaukin Sakkwato).
Sauran su ne: Malama Hauwa’u (Umma),
Malama Hadiza  (‘Yajjari), Malama Fadimatu ( Rigo), Malama Umaimatu,
Malama Hafsat da kuma Malama Sa’adatu.
Ta bar jikoki sama da 50 da kama kunne.
Gwamna Aminu Waziri Tambuwal da Sarkin musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar suna cikin wadanda suka haƙarci sallar janazar.
Sun roki Allah ya gafartawa margayiyar ya isarwa bayanta.
An yi sallar janazarta a masallacin jumu’a na Sarkin Musulmi Muhammad Bello dake fadar Sarkin musulmi a birnin jiha.
Ɗimbin jama’a sun halarci janazar margayiya tare da yi mata addu’ar samun gafarar Allah da aljanarsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *