Spread the love
Bayan matsi daga wasu masu kishin matasa  Sakkwato ta biya kudin jarabawar WAEC da NECO
Gwamnatin Sakkwato ta biya sama da miliyan 748 kuɗin jarabawar ƙare sikandare  WAEC da NECO.
Kwamishina a ma’aikatar furamare da sikandare Dakta Muhammad Bello Abubakar Guiwa ya sanar da hakan ya ce kuɗin na jarabawar  NECO 2019 da kuma WAEC da NECO 2020 ne.
Ya ce duk ɗaliban da suka rubuta jarabawar suna iya tafiya kan yanar gizo su duba sakamakon jarabawarsu.
Dakta Guiwa ya ce da wannan cigaban ɗaliban za su iya neman gurbin karatu a manyan makarantu cikin lokaci.
Haka ma ya kira masu ruwa da tsaki su cigaba da tsaya kai da fata don ka da ƙoƙarin gwamnati ya tafi ga banza.
Ƙungiyar masu kishin Sakkwato wadda Honarabul Malami Muhammad Galadanchi wanda aka fi sani da Bajare  ke jagoranta ne suka yi ta matsa lamba ga gwamnatin Sakkwato kan ta biya kuɗin jarabawar na yara, har sai da suka yi yunƙurin biyan kuɗin gwamnati ba ta nuna rashin gamsuwa da hoɓɓasar.
Ba su ƙyale ba sun ci gaba da abin matsalar kafin sanar da wannan mataki na gwamnati.
Bajare ya samu nasara ga wannan yunƙuri nasa ganin  yanda ya yi matsin lamba har  aka biya kuɗin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *