Spread the love

Akwai fargaba a jihohi reshen jam’iyar APC kan mamaye aikin bayar da rijistar APC da aka soma a wannan satin kamar yadda manema labarai suka fahimta.

Rahotannin da Managarciya ta samu na nuna cewa jagororin jam’iya a jihohi musamman wadan da ke da kudiri a siyasar 2023 sun fito kai tsaye da karfinsu suna kokarin mamaye aikin sai yanda suke so, za a yi abin da yake jefa fargaba a tsakanin mambobin jam’iyar kan cewa har yanzu ba za ta canja zane ba.

Domin soma fara aikin a jihohi masu ruwa da tsaki sun yi zama domin rufe duk wata kasawa dake tattare da aikin.

Bayanin da ke hannun Managarciya za a fara bayar da katin a jihar Kebbi da Filato da Ondo da sauransu za su fara ne a yau Talata.

A jihar Kebbi an gargadi masu kudi kar su mamaye aikn don yin hakan ba zai taimaki jam’iyar ba.

A jihar Lagos an samu rabuwar kai sosai abin da ake ganin zai kai ga samuwar shugabannin biyu a bangaren kowane mataki na jam’iyar, hakan na nuna APC a jihar Lagos za ta rabu biyu nan gaba kadan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *