Spread the love
Daga M. A. Umar, Minna.
An bukaci iyaye musamman matasan da ke jefar da ‘yayansu bisa dalilin samun su ta hanyar da bai da ce ba, ko kuma kan wani lalura na daban, Rabi’atu Sulaiman Yahaya Babangida ce ta yi kiran a lokacin da ta ziyarci gidan marayu da ke Minna dan tallafa masu da kayan abinci da bukin taya murnar haihuwa ga Amina Abubakar Lolo wata marainiya ‘yar shekara daya da haihuwa.
Rabi’atu ta cigaba da cewar ranar da mu ka taho ziyara a wannan gida, bayan komawata gida tausayin su ya hana min samun natsuwa da kai ga na nemi mahaifina ya taimaka min dan in kawo dan  tallafi ga  bayin Allah, na samu amincewar mahaifina akan bukatata wanda a yau Amina Abubakar Lolo take cika shekara daya da haihuwa na ga bukatar lallai in zo dan taya ta murnar wannan rana da bada tallafin abinci gare su.
Ina jin tausayin su, domin su ma mutane ne kamar kowa amma ba su da gata kamar yadda muke da shi ba kuma dan sun yi laifi ba sai dan son zuciyar da mahaifansu suka sanya kan su ya jefa su a wannan halin, ya kamata mu ji tsoron Allah mu sani duk wanda ya jefa rayuwar wani akan abinda bai da hakki akansa sai Allah ya tambaye shi. A kowani lokaci na tuna da marayun nan hankalina na tashi ganin irin halin da suka samu kan su, wanda ba laifi su kaiwa Allah ya jarabce su da wannan.
Ya kamata mu tausayawa rayuwar wadannan bayin Allah, mu sani halin da suka samu kan su ba zabin su ba ne, mu rika ziyartarsu muna taimaka masu domin ba san abin da Allah zai mayar da su ba a gaba ba. Masu haihuwar yara suna watsarwa da su ji tsoron Allah su daina, in har ba za ka iya daukar dawainiyar yaro ba kar ka yi sanadin zuwan shi duniya.
Halima Yakubu Ndanusa na daya daga cikin aminan mahaifiyar Rabi’atu, tace yau bayanin Rabi’atu ya sanya kowa kuka a wajen nan sannan kuma ya kamata mu tausayawa wadannan yaran tabbas a halin da muka same su abin a tausaya ma wa, su ma ‘yan Adam ne kamar kowa amma rashin gata da rashin sanin hakkin dan Adam ya sa iyayen su watsi da su, kamar yadda rahotanni suka nuna akwai wadanda tsintar aka yi, akwai wadanda sakamakon wani rashin fahimtar iyaye ne ya kawo su nan.
Kamar yadda wannan yarinyar Allah ya bata irin wannan zuciyar na tausayi da kwarin guiwar neman tallafin iyayenta dan ta taimaka ma wadannan bayin Allah, mu kan iyaye wannan izina ce gare mu na dunqule xan abinda mu ke samu na kayan abinci da sutura dan taimaka ma wadannan bayin Allah.
Alhaji Sulaiman Yahaya Babangida ( Cikasoron Minna) shi ne mahaifin Rabi’atu, yace lokacin da yarinyar tazo min da wannan buqatar na yi godiya ga Allah ganin ‘yar autata Rabi’atu, “yar kimanin shekaru tara da haihuwa ta zo min da irin wannan buqatar abin a duba ne kuma a tabbatar ma ta da burinta.
Da farko dan qarfafa guiwarta na sanya dukkanin yaran nan marayu an masu sabon dunki dan taya Amina Abubakar Lolo murnar wannan rana ta cika shekara daya da haihuwa, na biyu mun bada abinci da lemun roba da ruwan sha saboda tallafa ma wadannan marayun.
Wannan rana, ranar farin ciki ne da jin dadi a gare ni ganin jinin jikina tana son ta gaje ni a wajen taimakon jama’a, to Allah ya cika mata wannan burin ya daukakata a rayuwa da sauran ‘yan uwanta musamman ganin sun xauko turba mai anfani da inganci na taimakon jama’a domin wannan ya nuna suna goyon bayan ayyukan da na ke yi.
Jama’a da dama dai ganin muhimmancin wannan abin sun tallafawa gidan da kudade da alqawurran cigaba da kawo tallafi ga marayun.
Gidan marayun wanda gwamnatin Neja ta sabunta shi da gini irin na zamani a qarqashin gwamnatin Alhaji Abubakar Sani Bello yana qarqashin kulawar ma’aikatar mata da walwalar jama’a ne.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *