Sabon katin jam’iyar APC da duk dan jam’iya zai karba an fara karbar shi a jiya Assabar shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatarwa magoya bayan jam’iyarsu nada ‘yan takarar kowace kujera a kananan hukumomi ko matakin jiha ba za’a yi shi a Abuja ba wannan marar ta nada mutum daga Abuja ta kare a APC. Hakan ke nuna ‘yan siyasar Abuja tasirinsu ya kawo karshe fitilarsu za ta dusashe.

Buhari ya yi magana a mahaifarsa ta Daura a jihar Ktsina ya ce lokaci ya yi da jam’iyar APC ta zama ta mutane ce suke da tacewa kanta a kowane mataki.

Ya gargadi shugabanni da mamaye katin jam’iya a bari kowa ya karba.

Wurin yanka katin shugaban riko na jam’iyar da shugaban majalisar dattijai da Gwamnoni da sauran manya a jam’iyar sun halarci taron.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *