Spread the love

Hatsarin mota a jiya Assabar ya kashe akalla mutum 20 a jihar Kwara.

Mutane sha bakwai daga cikinsu sun kone ta yanda ba za a iya gane su ba, hatsarin ya faru ne a unguwar Olokonla kan hanayar Bode-Saadu a Jabba a karamar hukumar Moro a jihar ta Kwara.

Mutum daya  ne kawai ya tsira a hadarin ya ce bai samu wata goguwa ba.

An gano lamarin ya faru ne kan yawan gudu da tukin ganganci, abin ya faru da karfe 3am na dare akan motoci guda uku.

Shugaban hukumar kiyaye hadurra ta jihar Kwara ya tabbatar da faruwar lamarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *