Spread the love

Gwamnonin APC su hudu na son su tsayar da Jonathan takara a 2023

Yunkurin tsayar da tsohon shugaban kasa takarar shugaban kasa ga wasu gwamnonin APC su hudu daga Arewa ke yi zai canja lissafin siyasar Nijeriya.

Manema labarai sun fahimci hakan an kuma kungiyar ‘yan siyasa 10 daga kuduncin Nijeriya da wasu manya a jihar Bayelsa mahaifar tsohon shugaban kasar an basu dama su fara yekuwa a kafafen yada labarai don cimma manufa.

Kungiyar wadda wani jigo a jam’iyar APC kuma daya daga cikin mutanen Jonathan daga Bayelsa ya ce sun yi zama har sau biyu don a fito da hanyoyin yadda kamfen zai tafiya.

Wata majiyar a natsanake ta ce gwamnonin Arewa suna son Kudu maso Kudu su fara gudanar da kamfen sai su karfafa masu har a ciwo kan APC ta bayar da takara ga Jonathan.

Majiyar ta ce abin da ake son a fito da shi yekuwar a bari wannan bangare ya cika wa’adinsa a shekarar 2023.

Wannan shiri ana kitsa shi ne da zimmar a bayan ya kammala wa’adinsa mulki ya koma arewa.

Majiyar ta nuna gwamnoni huɗu ne a Arewa ke da wannan shirin amma zuwa yanzu ba a bayyana su ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *