Spread the love

 

A ranar  Juma’a data gabata ne bayan kammala sallar JUmu’a a  masallacin Juma’a na Al-Noor dake titin IBB Wuse 2 Abuja an kama wani Barawo da ya sace kudin Sadaki a dai-dai lokacin da ake daura Auren wata budurwa da Saurayinta, in da ya sade da mahalarta auren.

 

Bayanai  sun nuna  cewa, sadakin ya kai Naira 100,000.

An yi nasarar kama barawon da amsar sadakin a hannunsa  amma ya sha duka a hannun jami’an tsaron  masallacin.

Wannan shi ne karo na biyu da aka taba sace kudin sadaki a  masallacin an  sace  kudin kafin a biya sadakin wanda ya yi sanadiyar daura auren bashi sai daga baya angon ya sake samsun kudin ya biya sadaki.

Ba za a iya gane ko wannan barawon shi ne wanda ya yi na farkon ba sai dai shi wannan dubunsa ta cika, kuma a wurin ya gane kuskurensa saura da mi a kara kiyaye masu shiga da fice a masallacin da sauran wuraren ibada.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *