Honarabul Abdullahi Balarabe Salame dan majalisar tarayya dake wakiltar kananan hukumomin Gadabawa da Illela, yana cikin wadan da suka nuna sha’awar tsayawa takarrar gwamna a Sakkwato cikin jam’iyar APC ya ketare rijiya da baya a daren jiya Alhamis.

Salame a zantawarsa da manema labarai  a gidansa dake unguwar Bado ya ce “Jiya ina barci da misalin uku na dare mai dakina ta kirani ta ce ni ne na bude taga nace a’a tace akwai barayi cikin gidan nan.

“Ashe barayin sun shigo sun balle babbar kofar gida (gate), sun ba mai gadi kashi har sun barshi kwance, sauran mutane dake harabar gida sun boye.” a cewarsa.

Ya ce ko  da matar ta gaya masa ashe ‘yan bindigar sun yi kokarin bude kofa sun kasa sai suka rika harbi, ‘da na ga haka nima ina da tawa bindigar sai na dauko har na harbi daya daga cikinsu don kare kai da suka ga babu nasara suka dauki dan uwansu, suka tafi, bayan sun tafi ‘yan sanda suka zo.

‘”Wadanda suka gansu sun ce sun kai su 20 da bindigogi da adduna da yukake da makamai daban-daban. Sun daure ‘yan banga dake gadin unguwar kafin su shigo.”in ji shi.

Da ya juya kan harkar siyasar da yake yi ya ce Wannan ba zai karye min guiwa ba a matsayina dan siyasa ɓarayi ne ko wasu ne daban aka turomin don su salwantar da rayuwata domin tafiyar da muka dauko hakan ba zai razanani ba domin tafiya ce bani kadai ke cikinta ba ko bayana wani zai ci gaba.

Wata mai kama da wannan wasu ɓarayin ɗauke da makamai sun shiga cikin badon in suka kashe wani mai gadi tare da raunata wani magidanci bayan sun karɓi kuɗi hanunsa.

 

Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda ASP Muhammad A. Sadiq ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce hukumar su na sane da yukurin  fashi da makami da aka yi a unguwar Bado.

Ya ce hukunar na cigaba da bincike kan lamarin don haka mutane su kwantar da hankalinsu, kuma suna buƙatar haɗin kai domin gano waɗanda suka yi wannan aika-aikar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *