Spread the love
‘Yan bindiga sun aje makaman su sun rungumi shirin sulhu a zamfara.
Daga Aminu Abdullahi Gusau
Shirin sulhu da ‘yan bindiga dadi wanda gwamnatin Zamfara ta ke yi,i tun shigowar gwamna matawalle b isa karagar mulki, domin rage sace sacen jama’a don  biyan kudin fansa, da da kuma satar shanu da dai sauran su,  ya fara haifar da da mai ido. Domin yanzu haka ‘yan bindiga kimanin su bakwai sun ajiye makaman su kuma sun rantse ba za su kara yin wannan ta’ddanci ba.
Akan wannan tubabbin  ‘yan ta’addan da  suka tuba, suka mikawa gwamna matatwalle bindiga kirar AK 47 har guda goma sha hudu, hadi da albarussai masu yawan gaske a fadar gwamnatin jihar.
Da yake jawabi wajen taron kwamishinan sha’anin tsaro da harkokin cikin gida na jihar zamfara, Alhaji Abubakar Dauran (Justice),  ya ce wannan shirin sulhun ya samu gagarumar nasara domin tun cikin  watan shidda na shekara  2019 zuwa yau, an samu nasarar karbar bindigu har guda  148, da kuma albarusai kimanin  1418, aka karba  daga hannun yan ta’addan da suka rungumi shirin zaman lafiya.
 Dauran ya kara da cewa, an kubutar da mutun  1000 wadanda aka yi garkuwa da su,ba tare da biyan kudin fansa ba. Haka zalika yace wasu manyan ‘yan bindigar duk sun tuba kuma sun rungumi wannan shirin, kuma yanzu haka suna nan suna tafiyar da al’amurransu kamar yanda yakamata.
  Da yake karbar tubabun yan bindigar Gwamna  Bello Matawalle ya ce wannan ranar tana daya daga cikin ranakkun da baya taba mantawa da itaba.
Ya kara da cewa da yardar Allah nan bada jimawa ba wasu zasu kara kawo kansu domin su rungumi zaman lafiya, ya basu tabbacin cewa, duk wanda ya tuba to gwamnati zata yafe masa, kuma ta kawo shi cikin mutane masu albarka.
Gwamnan ya kuma basu tabbacin kare lafiyar su da kuma dukiyoyin  su.
Matawalle daga nan sai yayi kira da kada su yarda wasu bata gari suyi amfani da su domin wajen yin ta’ddan ci.
Daga karhe ya roki yan jarida dasu bidi karin bayani ga jami’an tsaro a duk lokacin da aka samu wanib hari na yan bindiga kafin rubuta labarin su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *