Spread the love

Rundunar sojojin da aka tura yankin farko na tawagar sun iso a hukumancegwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa’i ya karbe su, a Laraba ne rundunar ta bayar da sanarwar tura mata sojoji  300 kan hanyar domin magance yawan aiyukkan ta’addanci a hanyar ta Kaduna zuwa Abuja kamar Garkuwa da mutane da sauran aiyukkan ta’addanci.

Wannan cigaban ya zo wa mutanen kasa musamman farar hula da ban mamaki cewa wace irin hikima ce rundunar sojan ke son amfani da ita a wurin yakar ‘yan ta’adda a turo mata zalla a wurin yakarsu.

Wannan lamarin ba a saba da shi ba a kasar musamman a yakar ‘yan ta’adda komine ne hikimar haka mutanen kasa fatarsu sojojin kasa mata da maza su samu nasara a duk in da aka tura su don tsare kasa mutane da dukiyoyi domin dawo da cikakkaen zaman lafiya a kasa baki daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *