Spread the love
  • Gwamnan Neja ya rantsar da Sabbin Manyan Sakatarorin Gwamnati
Daga M. A. Umar, Minna
Gwamnan Neja, Abubakar Sani Bello ya rantsar da manyan sakatarorin gwamnatin jihar guda goma, inda ya nemi su aiki bisa rantsuwar da su ka yi a lokacin aikin ofisoshin su.
Gwamnan ya bayyana hakan ne jim kadan da kamnala rantsuwar da alkalin kotun majastare ta daya Hajara Baba tayi a madadin alkalin alkalan jihar, mai shari’a Aisha Lami Bawa Bwari wajen rantsar da su.
Gwamnan ya shawarci sabbin manyan sakatarorin da suka karvi rantsuwar da su zama masu tsantseni da kiyaye ka’idar aiki kuma su tabbatar suna aiki kafada da kafada da kwamishinonin su dan samun sakamako mai inganci.
Yace rantsuwar da suka dauka a yau, da su sani sun rataye wuyan su ne wajen daukar nauyin da ya rataya a wuyan su na tabbatar da jagoranci na gari.
” Dangane da rantsuwar da ku kayi, ban san mutum na wa ne hankalin su ya tafi akan alkawalin da ku ka yi a lokacin rantsuwar ba amma ina ba ku shawara da ku sake bibiyan abinda ku ka fadi domin samarwa kan ku mafita ga alkawalin da ku ka dauka”.
” Ina mai tabbatar maku cewar abinda ku ka karanta yayin rantsuwar zai iya kai jihar ga cigaba da kasa baki daya, kuma zai iya kare maku mutuncin ku”.
Gwamnan ya roki Allah da ya jagorance su, ya ba su kwarin guiwa dan samun nasarar yin wa’adin su a wannan kujerar.
Da suke zantawa da manema labarai bayan kammala rantsuwar, Malam Nuhu Garba Ngaski, babban sakataren ma’aikatar kula da kananan hukumomi, da Alhaji Hassan Baba Etsu, sakataren dindindin a hukumar RAMP sun bayyana cewar nauyi ne ya rataya a wuyan su, za su tabbatar sun manufofi da ka’idodin jihar wajen gudanar da aiki.
Za su tabbatar sun sadaukar da lokuttan su dan yin aiki mai inganci a dukkanin ma’aikatun su da jihar baki daya.
Manyan sakatarorin da aka rantsar sun hada da Hajiya Hauwa Isah Wali, da Muhammed Musa Nahauni, sauran sun hada da Gyiwodeyi Francis, sai Barista Hassana Danlami Idris Abdullahi Legbo, da Tanimu Yunusa, Nuhu Garba Ngaski, da Zakari Iliyasu Musa Sadiq, da Hassan Baba Etsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *