Spread the love
COVID-19; Gwamnatin Neja Zata Tilasta Anfani Da Takunkumi  Ko Biyan Tarar Dubu Biyar Ga Duk Wanda Aka Cafke
Daga M. A. Umar, Minna
Gwamna Abubakar Sani Bello ya umurci kwamishinan shari’a na jihar da ya shirya dokar musamman na tilasta anfani da takunkumin fuska ga kowa a jihar saboda kaucewa yaduwar annobar COVID-19 a jihar.
Umurnin ya biyo bayan shedawa gwamna ayyukan kula da annobar COVID-19 da halin da ake ciki akan annobar a jihar wanda kwamitin ya yi.
Gwamna Sani Bello ya ce dokar za ta fara aiki daga ranar littinin daya ga watan fabrairun 2021, inda yace sake garkame jihar ba mafita ba ne duba da halin da tattalin arziki ke ciki yanzu, anfani da takunkumin fuska zai zama wajibi kuma za a kafa kotun tafi da gidan ka dan hukunta wanda aka samu da taka dokar nan ta ke tare da biyan tarar dubu biyar.
Gwamnan ya umurci cewar ma’aikatan musamman ne kawai ke da ikon shiga gidan gwamnati da kuma ofisoshin gwamnati, wadanda shugabannin ma’aikatun gwamnati da sassan ma’aikatun da kuma wuraren ayyuka na musamman.
Ya kuma kara da cewar kwamitin su hada hannu da jami’an tsaro har da jami’an da ke kula da tuki da sauran jami’an sintiri dan tabbatar da an bi wannan dokar.
Gwamnan ya umurci bukatar wayar da kan jama’a da dukkanin kungiyoyi a jihar da kuma kafafen sadarwa ta hanyar anfani da dukkanin harsuna wajen wayar da kan jama’ar jihar, akan bukatar jama’a su kara sanin muhimmancin kaucewa yaduwar annobar, dan kiyaye kai da kulawa wajen kaucewa yaduwar annobar a jihar.
Ya baiwa kwamitin shawarar baki masu shigowa jihar akwai bukatar yi masu gwaji za a caje su naira dubu ashirin.
Da yake bayani a madadin kwamitin kula da annobar a jihar, kwamishinan lafiya, Dakta Muhammed Makusidi, yace zuwa yanzu jihar na da adadin mutum 695 da aka tabbatar sun kamu a yankunan kananan hukumomi 22 cikin 25 da jihar ke da su, wanda zuwa mutum 14 annobar ta kashe, inda ya kara da cewar daga cikin rahoton 16 da aka samu na masu dauke da annobar 15  yan yiwa kasa hidima ne.
Kwamishinan yace cibiyar binciken annobar da ke babban asibitin Minna ta fara aiki tun cikin watan Satumbar 2020, daga cikin kalubalen da cibiyar ke fuskanta tun bayan kafata, shi ne rashin bin dokokin kiwon lafiya da kuma ya janyo rashin cigaba da aikin wanda ke lakume makuddan kudi kowani wata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *