Spread the love

 

 

Rikici ya barke  a daki na 028 dake cikin harabar majalisar tarayya ta kasa, in da aka shirya taron tattaunawa da jama’a kan dokar kamfanin man fetur PIB tsakanin wasu suka halarci zaman taron a zauren Majalisar dokokin tarayya.

 

Bayanai na  cewa har yanzu ba’a gane wadanda suka tada rikicin ba amma ana kyautata zaton wasu ‘yan jihohin yankin Neja Delta ne gefen dake da albarkatun man.

Rikicin ya barke da tsakiyar ranar yau Alhamis ne lokacin da shugaban kwamitin, Hanarabul Mohammed Munguno, ya yi kira ga ‘yan jihohin Neja Deltan su gabatar da jawabinsu.

Kawo yanzu, ‘yan majalisa da sauran wadanda ke halarci a wajen sun gudu daga dakin gudun kada wani abu ya same su mai muni.

Ana samun fargaba matuƙa a duk lokacin da aka samu ɓarkewar rikici a zauren Majalisar dokoki, a mafiyawancin lokuta rikicin na faruwa ne tsakanin ‘yan Majalisar da junansu.

Sai dai ana ganin wannan rikicin ya sauya salo domin rikici ne da ya faru tsakanin wasu baƙi da suka halarci zaman majalisar.

Har ya zuwa lokacin rubuta wannan rahoto dai ba a tantance ainihin gaskiyar abin da ya haifar da rikicin ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *