Spread the love
Wutar lantarki ta kashe wani ɓarawon waya a jihar Kebbi
Wutar  lantarki ta kashe ɓarawon waya  a kan transfoma a garin Bunza cikin ƙaramar hukumar a jihar Kebbi
Bayanai sun nuna cewa ɓarawon yayi nasarar kwance waya biyu yayin da yake ƙoƙarin kwance ta 3 sai wutar lantarki ta dawo abin da ya yi sanadin rasa ransa da ya yi.
Mutane sun zo kallon wannan  ikon Allah wannan ɓarawon ya yi niyar sanya garin cikin duhu ashe shi ne zai barin duniya gaba daya.
Har yanzu hukumomin da abin ya shafa ba wanda ya yi magana kan abin da ya faru.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *