Spread the love

Bagudu ya ba da umarnin a rabawa manoma takin zamani a mazabu  225 na Kebbi

Gwamnan Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya bayar da umarni da gaggawa a cigaba da sayarwa manaoma takin zamani a dukkan mazabu 225 dake jihar Kebbi.

Gwaman ya aika ton 30 ga kowace mazaba a jjihar Kebbi, ya umarci KASCOM  ta hada da masu ruwa da tsaki daga cikin kananan hukumomi da mazabu don cimma nasarar sayar da takin, manoman gaskiya nada bukatar takin domin kara bunkasa harkar noma a jihar.

A bayanin da Dakta Sani Danjuma ya sanyawa hannu ya ce wadanda za su sanya idanu ga sayar da takin Kwamishina da dan majalisar dokoki da shugaban karamar hukuma da malamai da sauransu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *