Spread the love

 

Wata annoba ta bulla a jihar Sakkwato a unguwar Helele cikin birnin Sakkwato har ta yi sanadin mutuwar mutum hudu an kai wasu 30 asibiti daban daban a jihar jihar.

Cutar wadda aka danganta da ciyon amai da gudanawa ne ya samu mutane ta hanyar ruwan da suka sha ko suka yi amfani da su.

Gwamnan Aminu Waziri Tambuwal amadadin gwamnatin Sakkwato ya jajantawa mutanen da suka rasa danginsu da wadan da aka kwantar a asibiti saboda cutar da bulla a unguwar.

 

 

Ya ce gwamnati ta samu labarin bullar cutar da ta yi sanadin mutuwar mutum hudu, aka kwantar da mutum 24 a asibiti, don haka gwamnati ta sanya kwamitin kwararri karkashin jagorancin kwamishinan lafiya da muhali don su gano musabbabin cutar da maganinta.

Haka ma Tambuwal ya ce gwamnati ta dauki nauyin maganin wadan da suka harbu da cutar ya yi masu fatan samun sauki su koma cikin danginsu

Ya yi kira da akwantar da hankali kuma mutane su rika kula da tsafta musamman a wannan lokaci da ake fuskantar kalubale daban-daban.

 

Gwamnan a wani jawabi da ya fitar da kansa ya roki Allah ya gafartawa wadan suka rasu ya tsare wadanda ba su kamu ba.

Sardaunan matasan Sakkwato Alhaji Mujitaba Isah Helele ya ce daga baya an fahimci annoba ce da ta faru kan shara da mutane ke watsarwa barkatai da wasu kananan yara da ke yin kashi barkatai yanda suka ga dama wanda hakan na shiga cikin bututun ruwa da mutane ke sha.

Ya godewa maigirma gwamna kan kwamitin da ya kafa domin gano musabbabin annobar da matakin da za a dauka kai tsaye, da kula da wadan da ba su da lafiya kan cutar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *