Spread the love

 

Daga Muhammad M. Nasir

Kananan hukumomin Sakkwato ta kudu data Arewa tun da aka fara dimukuradiya a Nijeriya aka samar da majalisar wakillan tarayyar Nijeriya ake wakiltarsu a zauren majalisa, amma a kowane lokaci bayan kammala zabe suna da tambayar da suke yi wa kansu, ba a samu amsar wannan tambayar ba sai a wannan marar da ake tun karar zaben 2023.

Al’umma a kwaryar birnin Sakkwato da kewaye a duk sanda suka samu labarin cigaba da wasu wakillai a majalisar tarayya suka aiwatar ga jama’arsu a kananan hukumomin da suke wakilta, sai ka ji suna tambayar kansu ‘yaushe ne kananan hukumomin Sakkwato ta kudu da ta Arewa za su mori wakilci a majalisar tarayyar Nijeriya?’.

Wannan tambayar da kowane dan asalin kananan hukumomin suka hardace suke tilawatar kullum ta sanya daya daga cikin masu kishin jama’a da son taimaka musu waton INJINIYA ALMUSTAFA KOFAR MARKE ya kudiri aniyar share hawayen mutanen yankin nasa, ganin ko ba komai yadda wajabtawa kansa abinsa na al’umma ne, ba wani dalili da ba zai zamar musu dan aike ba, da zai karbo hakkinsu ya ba su.

Injiniya Almustafa sunansa ya shiga kusan kowane gida a cikin garin Sakkwato saboda dattakonsa da alhrinsa da burinsa na ganin mai rauni ya samu karfi, mai nema ya samu, uwa uba shi gatan maraya ne, kuma bango ne majingimnar kowane mabukaci kan haka ake kiransa da ‘DAMINA UWAR ALBARKA’.

Soyayyarsa ga matasa wata baiwa ce da Allah ya ba shi ba ya son ya ga matashi a zaune ba harkar da yake yi, ya tsani maula da bangar siyasa hakan ya sa ba ya wasa wurin samarwa matasa aikin yi da kuma sana’ar dogaro da kai.

Kofar Marke kyauta ce Allah ya baiwa al’ummarsa wadda bai kamata duk wani mutum mai hankali da sanin yakamata ya bari ta subuce masa ba dole ne a zo a hada kai wuri daya ba zancen bambancin jam’iya a tabbatar da wakilcin wannan bawan Allah kamar yadda alherinsa ya shiga hannun kowa ba tare da ware dan wata jam’iya daban ba.

Ba wata al’umma mai son cigaba da kokarin magance matsalolinta za ta samu mutum irin Injiniya Almustafa ta yi wasa da shi, ya zama wajibi a goya masa baya ya wakilci jama’a ko ba komai hidimtawa mutane a cikin jininsa yake, ba wata rana da ba zai share hawayen mabukaci ba tare da la’akari da kowane bambacin abu na rayuwa ba. Tallafi, jinkai da taimakawa mutane su ne ruwan shansa a kullum, duk mai yi ba don neman biyan bukata a wurinka ba, shi yafi dacewa ka sanya a gaba. Injiniya cancantace ne har a wurin wanda ba jam’iyarsu ta APC daya da shi ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *