Jamíyar PDP a mai adawa a Nijeriya ta bayyana nada sabbin hafsoshin tsaro da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi a wannan lokacin da cewa an makara saboda kasar ta shiga halin kaico a sha’anin tsaro.

PDP ta ce sai da komi ya lalace sannan aka canja hafsoshin tsaron hakan ke nuna yanda shugaba Buhari yake da kin karbar shawara hakan na kara jefa kasar cikin kamayamaya.

Ta ce duk da hakan dai jam’iyar na sa ran sabbin hafsoshin za su dage damtse na ganin sun yi maganin kalubalen da kasar ke fuskanta, da nazarinsu da dagewa kan aikinsu zaman lafiyar kasar zai iya dawowa.

PDP ta yi kira gare su da su sadaukar tare da hobbasar dawo da martabar sojoji da kimarsu a cikin alúmma ta hanyar yakar rashawa da cin zarafin al’umma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *