Spread the love
Daga M. A. Umar, Minna.
An bayyana cewar wajibi ne gwamnati ta kara kaimi wajen lalubo hanyoyin da za a kawo karshen zubar da jini a kasar nan ta hanyar samar da gurabun ayyuka ga matasa.
Limamin masallacin juma’ar jami’ar kimiyya ta tarayya dake Minna ( FUT), Dakta Bashir Ahmed Usman Yankuzo ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Minna.
Dakta Bashir ya cigaba da cewar wannan matsalar tsaron wani annoba ne amma rashin aikin yi ga matasa ya kara assasa shi, wanda dole ne jama’a su rungumi addu’o’i ita kuma gwamnati ta lalubo hanyar kawo karshen wannan lamarin ta hanyar kirkiro hanyoyin ayyuka ga matasa.
 Yankuzo ya kara da cewar akwai kungiyoyin addinai da dama da gwamnati za ta iya hada kai da su wajen inganta rayuwar matasa ganin irin yawan matasa mabiya da suke da su, duk irin shirin cigaban matasa na horar da su ayyuka idan ana anfani da kungiyoyin addinai za a iya cinma nasara domin sun san hanyoyin da ya kamata su bi wajen ganin matasan sun anfana.
Sana’a da ilimi suna tafiya ne kafada da kafada wanda rashin sana’a ko aikin yi na iya jefa dubban matasa cikin hadari.
“Ina yabawa kokarin da gwamnati jiha ke yi amma akwai bukatar kara kaimi wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a”. a cewarsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *