Spread the love
Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya aminta da takardar murabus da shugabannin tsaron ƙasa suka gabatar masa.
Shugabanin tsaron sun haɗa da shugaban tsaro dana sojojin sama dana ruwa dana ƙasa General Abayomi Olonisakin; da  Lt-Gen. Tukur Buratai; da Vice Admiral Ibok Ekwe Ibas; da Chief of Air Staff, Air Marshal Sadique Abubakar.
Shugaba Buhari ya gode wa tsoffin shugabannin sojojin kan nasarorin da aka samu a wurin yaki da ta’addanci a Nijeriya.
Sabbin da shugaba Buhari ya naɗa su ne shugaban tsaro Major-General Leo Irabor, Shugaban sojojin ƙasa Major-General I. Attahiru; Shugaban sojojin ruwa Rear Admiral A.Z Gambo; sai na sama Air-Vice Marshal I.O Amao.
Buhari ya taya sabbin murnar naɗin ya yi kira gare su da su zama masu sadaukarwa ga aikinsu a wannan damar da suka samu.
Wannan bayanin na ƙunshe ne a wani bayani da mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai Femi Adesina ya fitar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *