Mahara sun kashe shugaban karamar hukuma a  Taraba
Wasu da ake zaton  masu garkuwa da mutane ne sun kashe shugaban karamar hukumar Ardo-Kola da danuwansa  a jihar Taraba.
CiyamanSalihu Dovo da ɗan uwansa Timothy Aminu an sace su ne a gidan shugaban karamar ta Ardo-Kola dake anguwar Sabon gari  a cikin garin Jalingo da misalin karfe daya na daren Talata data gabata.
Bayan sun tafi da su da ɓatagarin suka fahimci ‘yan sand da ‘yan sa kai na biye da su sai suka harbe su  suka bar gawarwakin a wani kauye mai suna Nahuta dake hayin Kogin Lamurde.
Kakakin rundunar yansandan Jihar Taraba DSP David Misal ya tabbatar da aukuwan wannan lamari ya ce an kama mutane uku wadanda ake zargi da hannun a sacewa da kashe shugaban karamar hukumar ta Ardo-Kola.

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *