Spread the love

Daga Muhammad M. Nasir

Gwamnan jihar Sakkwato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya   kira ministan ‘yan sandan Nijeriya Alhaji Muhammad Maigari Dingyaɗi da kwamishinan lamurran  ‘yan sanda a lokacin da yake jero sunayen muhimman mutane da suke cikin tawagar shugaban ƙasa wadda ya aiko domin yi wa gwamnati da jama’ar Sakkwato jajen gobarar wuta da ta same su.

Tambuwal bayan ya ambaci sunan shugaban tawagar Farfesa Ibrahim Gambari da tsohon gwamnan Sakkwato Sanata Aliyu Wanakko da ministan sadarwa Ali Isah Pantami sai ya ce mai girma Kwamishinan lamurran ‘yansanda Muhammad Maigari Dingyaɗi Katukan Sokoto, zai wuce da ambaton suna na gaba aka an karar da shi kuskuren sai ya dawo ya gyara cikin raha har ya ƙara da ‘magajina’.

Gwamnan ya cigaba da jawabinsa da yin godiya ga shugaban ƙasa kan tawagar gwamnatin tarayya da ta zo domin jajantawa gwamnati da mutanen jiha amadadin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce gwamnatin jiha ta gano musabbabin tashin gobarar daga wutar lantarki ne a taranfomar da ke cikin kasuwar da ake huldar kasuwanci da ita a duk Afirika.

Tambuwal ya ce “Kusan shago dubu 16 ke cikin kasuwar kashi 60 nata ya kone a wannan gobarar abin damuwa ne a hasarar da aka yi ga mutanen jiha.

“Muna tsammanin tallafi ga gwamnatin tarayya musamman ga ‘yan kasuwar da suka yi hasara a cikin wannan yanayi na tsadar rayuwa.” a cewar Tmbuwal.

Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Farfesa Ibrahim Gambari ne ya jagoranci tawagar ya ce sun zo ne domin su jajantawa mutanen Sakkwato amadadin shugaban kasa, kuma su ga irin barnar da wutar ta yi.

Ya ce gwamnatin tarayya za ta taimakawa gwamnatin Sakkwato domin sake  gina kasuwar abin da zai ƙara haɓaka  kasuwanci a Nijeriya baki daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *