Spread the love
Almundahana Da Kuɗin Karamar Hukumar Shiroro; Wajibi A Kafa Kwamitin Binciken Shugaban Karamar Hukuma- Inji Masu Ruwa Da Tsaki
Daga M. A. Umar, Minna
Sakamakon wata taƙaddamar ruf da ciki da majalisar kansulolin karamar hukumar Shiroro ta kai ga korar shugaban karamar Hukuma-, Hon. Sulaiman Chukuba a karshen shekarar 2020, zuwa yanzu dai bayan shiga tsakani da wasu masu ruwa da tsaki su ka yi ya sanya canja matsayin majalisar kansulolin zuwa dakatarwa.
Bayan wani takardar korafi da majalisar kansulolin da wasu dattijan jam’iyyar APC suka rubutawa gwamna Alhaji Abubakar Sani Bello kan zargin ruf da cikin da kansulolin su ka yiwa shugaban karamar hukumar, inda gwamnan ya kafa kwamiti da za su binciki shugaban ƙaramar, Honarabul Sulaiman Chukuba tsawon wata daya ke nan kamar an aiki bawa garin su.
Sakamakon haka ne ya sa dattijai da masu ruwa da tsaki a karamar hukumar da su ka kunshi wasu tsaffin shugabannin karamar hukumar, da wasu masu rike da mukamin siyasa a matakin jiha, kiran taron manema labarai a yammacin lahadin makon nan mai karewa.
Alhaji Awaisu Muhammad Giwa Wanna, wanda yai magana a madadin dattijan APC, yace maganar zargi kan Honarabul Sulaiman Chukuba gaskiya ne, amma matsayin kora da kansulolin su ka yi da majalisar dokokin jiha ta nemi a mayar da shi dakatarwa har bayan kammala bincike mun gam su da shi, amma abin da mu ke cewa tun bayan da gwamna ya kafa kwamitin nan zuwa yau kimanin wata ɗaya ke nan, har yanzu ba ta zauna ko sau ɗaya ba.
Abinda ba mu fahimta ba shi ne, shin kuɗin da ake zargin Honarabul Sulaiman Chukuba da yin a won gaba da shi, da ‘yan kwamitin ne aka lashe su, da suke tsoron yin bincike dan gane gaskiyar lamarin.
Ko kuma naira miliyan sittin da tara da kansulolin su ka ce shugaban karamar hukumar yayi awon gaba da su ba gaskiya ba ne, ina batun sama da naira miliyan daya na kudin shigar da iyayen mu ke baiwa karamar hukuma da sunan haraji da karamar hukuma ke amsa da ba a san inda ake kashe su ba ya kwana.
Akwai batun miliyan hudu da dubu dari biyar na tsaron kasa da ofishin sakataren gwamnatin jiha da ma’aikatar kananan hukumomi ta amince a baiwa karamar hukumar Shiroro da a kullun matsalar tsaron kara hayyaka yake yi a Shiroron, muna bukatar wannan kwamitin da gwamna ya kafa ta binciko su.
A korafin kansulolin sun an bato batan naira miliyan dari biyu da saba’in da hudu wanda ya haifar da daukar matakin da kansulolin su ka dakatar da shugaban karamar hukumar Shiroro a ranar 29 na watan disambar 2020, bisa la’akari da kuri’a 11 cikin 14 na kuri’ar kansulolin.
Saboda haka maganar kunbiya-kunbiyan rufe wannan zargin ga Hon. Sulaiman Dauda Chukuba ba zai sabu ba, domin ba shugaban karamar hukumar da zai aikata irin wannan katobarar a ce a rufe shi, kuma ya cigaba da jagorantar karamar hukuma a haka.
Alhaji Akilu Isyaku Kuta, jigo ne a jam’iyyar APC a karamar hukumar Shiroro, yace mun ji an ce wai an turo kwamishinan wasanni yazo a sauna dan yin sulhu, to mu ba mu ki sulhu ba, amma a matsayin kwamishina na kasancewarsa dan asalin karamar hukumar Shiroro, ya fito ya fadawa duniya aiki guda daya da ya kawo a karamar hukumar tun hawansa wannan kujerar.
Sannan a haka ake son mu cigaba da kasancewa a karamar hukumar Shiroro, ba mu tafi jam’iyyar APC dan rashin gaskiya ba, mun tafi da tunanin kawo cigaba a karamar hukumar nan, ba fa yan jam’iyyar PDP ke korafi ba, balle a ce maganar adawa ce ba, mu ne dai ‘yan APC ke korafi kuma dole a dubi korafin mu dan ayi gyara mu samar da cigaba a karamar hukumar nan.
Ba za mu yarda maganar nan ta mutu haka ba, dole ayi bincike dan gano gaskiyar maganar domin daukar matakin da ya dace. Abin kunya ne a ce jam’iyyar da talakawan Shiroro sun bada lokacin su da rayuwarsu wajen kawo canji mai ma’ana da zai kawo cigaba a karamar hukumar Shiroro kuma ta fake da guzuma tana harbin karsana, za mu tsaya kai da fata wajen ganin mun kwato hakkin jama’ar mu, saboda ba za mu yarda da barin tarhi marar inganci da abin gori ga jama’ar mu ba.
Taron maneman labaran ya kunshi tsoffin shugabannin karamar da kuma masu ruwa da tsaki a jam’iyyar APC na karamar hukumar Shiroro.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *