Spread the love

Jam’iyar APC reshen jihar Imo tana jiran matakin da tsohon gwamnan jihar Rochas Okorocha ke shirin yi na samr da wata hadakar siyasa kafin ta bayyana matsayinta kan lamarin.

Shugaban riko na jam’iyar a jihar Marcon Nlemigbo ne, ya fadi hakan a zantawarsa da manema labarai ya ce su a yanzu goyon bayan shugaba Buhari da gwamnansu Hope ne a gabansu domin a samu romon dimukuradiyya ga al’umma.

Okorocha ya fadi a ranar Litinin data gabata a jihar Rivers lokacin da ya ziyarci Wike don  kaddamar da wasu aiyukka ya ce ‘Muna da mutane bata gari a APC hakanan ma akwaisu a PDP da wannan nake kira mi zai hana mutanen kirki ba za su hadu wuri daya su jagoranci al’umma ba”.

Shugaban ya ce Rochas a matsayinsa na dan kasar Nijeriya yana da ‘yancin ya fadi albarkacin bakinsa, sai dai su za su jira har sai ya aiwatar da abin da ya fada.

Ya ce sun sani ko da Rochas ko babu shi APC a Imo tana da karfinta don haka abin da ya fadi ba barazana ce gare su ba.

Kalaman Rochas sun nuna akwai alamun wasu mutane daga jam’iyar APC da PDP za su balle su samar da wata jam’iyar hadaka a Nijeriya tasirinsu ko akasin haka lokaci ne zai iya bayyana hakan.

Da kamar lokaci na neman ya kure masu wannan tunanin na samar da jam’iyar hadaka ganin yanda kakar zabe ke kusantowa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *