Spread the love

 

Wata kungiya a jam’iyar APC ta yi matsayar ba za su bari duk wani dattijo mai shekarru ya jagoranci jam’iyar ba.

“Mun yi zama sau biyu mun kai matsayar samar da sabuwar  kungiya da za ta tsaya ta ga an baiwa sabbin jini shugabancin jam’iyar APC. Ba mu bukatar  dan takararmu da zai tsaya a ce gwamna ne ko mataimakin gwamna ko Minista ko Babban Sakatare ko Ambasada ko babban darakta ko wani shugaba a wata ma’aikata, dukan wadan nan ba mu bukatar su jagoraci jam’iyarmu ta APC”. a cewarsu.

Sun ce suna bukatar sabon jini ne da bai taba rike wata babbar kujera ba, don haka ba su aminta da takarar tsohon gwamnan Zamfara Abdul’aziz Yari da tsohon shugaban jam’iyar PDP Sanata Ali Modu Shariff da tsohon gwamna Clement Ebri da sauransu ba.

 

“Haka ma duk wanda ya kai shekara 65 zuwa 70 har sama ba mu bukatarsa a jagorancin APC. Muna bukatar shugaba na kasa ba tare da durkusu ba hakan zai sa a jagoranci APC kamar kowace jam’iya a duniya.

“Kudirin da muke da shi kenan kuma mun sanar da duk wani mai ruwa da tsaki a jam’iyar har da gwamnoni domin a yi tafiya tare. Muna son matashi ne ya jagoranci jam’iyar saboda duk wadanda suka nuna sha’awar takarar dattawa ne, ba wani abu da za su kawo sabo ga tafiyar jam’iyar. Wasu daga cikinsu ma sun fara haduwa da kalubale domin a jihohinsu ana adawa da takararsu.

A lokacin da majiyar ke karba tambaya ga manema labarai ta ce a yanzu da nake magana da kai mun samu goyobn baya gwamna 12 a jamíyar APC da suka aminta a samar da matashi ya jagoranci APC.

Ya ce suna tafiyar ne a tsanake amma anan ba da jimawa ba za su yi taron manema  labarai don sanar mambobin jam’iyar APC matsayarsu, a yanzu suna neman shawara ne kan ra’ayin nasu na rashin bukatar duk wani tsohon shugaba a jagorancin.

Kungiyar ta ce “Mun yi farinciki da muka samu gwamna 12 na goyon bayanmu abin da ya rage mana mu samu shugaban kasa Buhari don yi masa bayani da sanya wa tunanin albarka na kawo sabon jini da sabon tunani a APC.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *