Spread the love

Jam’iyar APC a jihar Sakkwato ta yi matsayar shiga zaɓen ƙananan hukumomi da za a gudanar a jihar a ƙarshen watan maris.

Shugaban jam’iyar na jihar Sakkwato Alhaji Isah Sadiƙ Achida ne ya sanarwa Managarciya a waya cewa ba abin da zai hana mu shiga zaɓe matuƙar an sanar da mu a hukumance.

 

Ya ce jam’iyar APC za ta shiga zaɓen ƙananan hukumomi da za a gudanar Sakkwato ba abin da zai hana mu shiga.

Kafin wannan bayani a jihar an fara hasashen da wuya APC ta shiga zaɓen ganin yanda ake yi a sauran jihohi duk jam’iyar da ke mulki a jiha ita ce ke lashe zaɓe gaba ɗaya.

Managarciya na hasashen gwamna Aminu Waziri Tambuwal zai iya gudanar da sahihin zaɓe a jihar saboda burin da yake da shi na tsayawa takarar shugaban ƙasa, zai yi abin da takwarorinsa gwamnoni ba su yi ba na baiwa ‘yan adawa damar gwada farinjini da karɓuwarsu.

A wannan zaɓe Tambuwal zai ƙara haskaka tauraronsa a siyasar Nijeriya matuƙar labarin zaɓen Sakkwato ya bambanta dana sauran jihohin Nijeriya a fannin tsari da baiwa kowa damar gwada tasirinsa a siyasa.

Zaɓen zai nuna halin Tambuwal ga jam’iyun adawa wanda saƙo ne zai isa ga duk ɗan siyasa a Nijeriya zai fahimci Tambuwal daban ne da sauran ‘yan siyasa ko duka kanwar ja ce mai ƙarfi ke murƙushe maras ƙarfi ko ya ne lokaci zai fito da komai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *